Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bam Ya Jikkata Jami'an Tsaro Biyar A Maiduguri


Hoton wani soja yake aikin tsaro lokacin zabe.

Wani Bam ya tashi a dai dai lokacinda wata motar jami'an tsaro na hadin guiwa suke shirin fara sinitiri a titin Lagos, a birnin Maiduguri, cikin jihar Borno. Jami'ai biyar sun jikkata.

Alhamis din nan d a misalin karfe 7 na safe ne bam ya tashi a lokacinda wata motar jami'an tsaro na hadin guiwa,sojoji da Yansanda suke aikin sintiri a kan titin lagos,a birnin Maiduguri,babban birnin jihar Borno.

Mataimakin kwamishinan 'yansandan jihar,Alhaji Zakari Adamu wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin yace 'Yansanda uku da sojoji biyu ne suka jikkata sakamakon tashin bam din.

Da yake amsa tambayoyi,kwamishinan ya bada haske kan fada da aka gwabza da wasu da ya kira "bata gari,da basa son zaman lafiya" da suka kai wa ofishin 'yansanda dake unguwar tashar baga hari,a daren jiya.

Alhaji Zakari yace mutanen sun je ofishin ne cikin motocin golf uku suka bude wuta kan ,jami'an tsaron,wadanda basu bata lokaci ba suka mai da martani. Da suka ga anfi karfinsu sai suka gudu cikin gari.Aka bisu aka kama wasu wasu,wasu daga cikinsu.

Mataimakin kwamishinan 'yansandan yace ana ci gaba da bincike kan wan nan lamari.

XS
SM
MD
LG