Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bam Ya Tashi a Abuja Dazun Nan


Tashin Bam Yau Laraba a Banex Plaza na Abuja, Yuni 25, 2014.

Wani abu kamar bam ya tashi a kusa da wata kasuwar masu hannu da shuni a Abuja, babban birnin Najeriya.

Wani shaida ya fadawa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa sun ji wata kara mai karfi da ta farfasa tagogi, sai kuka ruga da gudu, kowa ma ya fara gudu.

Wani kakakin hukumar agajin gaggawa ta Najeriya, manzo Ezekiel, yace sun samu labarin fashewar wan nan abu da misalin karfe 4 na yamma a wani wuri mai suna Emab Plaza.

Wani rahoton da farko yace wannan abu ya fashe ne a wani wuri mai suna Banex Plaza.

XS
SM
MD
LG