Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bama-Bamai Biyu Sun Tashi A Kasuwar 'Yan Waya Ta Kano Yanzu


Rahotanni daga Kano na cewa wasu bama-bamai guda biyu sun tashi da misalin karfe 4:15 na la'asariyar yau a Kasuwar 'Yan Waya Dake Unguwar Farm Centre ta cikin birni.

Babu bayanin adadin wadanda suka mutu amma shaidu a wurin sun ce mutane da dama sun mutu.

Akwai alamun cewa wasu mata 'yan kunar bakin wake ne suka shiga da bam din, domin wani shaida yace an ga bangarorin jikin wata mace a warwatse a wurin, kamar dai abin a jikinta ya tashi.

jami'an tsaro sun killace wurin a yanzu haka.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG