Accessibility links

Bama-bamai sun tashi a kusa da tawagar masu sa ido na Majalisar Dinkin Duniya a Siriya

  • Ibrahim Garba

A iya hango dakarun Siriya daga tagar wata motar soja da bam ya yi wa illa

Wata fashewa ta bararraka wasu motocin sojojin da ke biye da tawagar

Wata fashewa ta bararraka wasu motocin sojojin da ke biye da tawagar jami’an sa ido na Majalisar Dinkin Duniya a Syria yau Laraba, kwana guda bayan da mai shiga tsakani na kasa da kasa Kofi Anan ya yi gargadin cewa cigaba da boren da ake wa gwamnati zai iya kaiwa gay akin basasa.

Fashewar, wadda ta auku a birnin Daraa mai fama da tashin hankali da ke kudancin kasar, ta raunata akalla sojoji 6. Jagoran tawagar jami’an sa idon, Manjo-Janar Robert Mood, na cikin tawagar to amman da shi Mood din da sauran jami’an sa idon babu wanda ya sami rauni.

Jami’an sa idon sun yi ta zirga-zirga a fadin Syria don ganin ko ana kiyaye yarjajjeniyar tsagaita wutar mai sarkakkiya, wanda hakan na daga cikin shirin zaman lafiyar da Mr Annan ya cimma.

A jiya Talata, Mr. Annan ya ce aikin sa idon da alamar shi ne kadai damar da ta rage ta samar da zaman lafiya a Syria. Bayan wani taron manema labaran da kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya kira, Annan ya gaya wa manema labarai cewa akawai matukar barazanar cewa idan ba a yi hakan ba to fa kasar na iya fadawa cikin yakin basasa.

A halin da ake ciki kuma gwamnati ta cigaba da kidaya kuri’un zaben ‘yan Majalisar da aka gudanar ranar Litini, wanda ‘yan adawa su ka yi watsi da shi a zaman shirme.

Kamfanin dillancin labarai mallakin gwamnati mai suna SANA y ace jami’ai a yankuna da dama, ciki har da Idlib da Daraa, sun kammala tattara kuri’u.

XS
SM
MD
LG