Accessibility links

Ban Goyi Bayan Shawarar Tony Blair Ta Janye tallafin Man Fetir ba-Jibril Aminu

  • Grace Alheri Abdu

Shugaban kasar Najeriya mai jiran gado Muhammadu Buhari, yayi Magana da ‘Yan Jarida Alokacin ziyarar tsohon Faras MInistan Birtaniya Tony Blair A Abuja, Nigeriya, Mayu 13, 2015.

Jawabin da tsohon firaiministan Birtaniya ya gabatar a wurin taron bita na APC a Najeriya ya bar baya da kura.

Tsohon minisan mai a Najeriyam, Farfesa Jibril Amiu ya bayyana cewa bai goyi bayan shawarar da tsohon firai ministan Birtaniya Tony Blair ya bayar ta janye tallafin man fetir ba.

A cikin hirarshi da wakilin sashen Hausa Hassan Maina Kaina a birnin tarayya Abuja bayan jawabin tsohon firai minisatan a wajen taron shata makamar aiki da jam’iyar APC ta shirya, Prof Jibril Aminu yace wanan shawarar ba alheri bane ga gwamnati mai jiran gado, illa ta jawo mata bakin jinni kawai.

Yace ‘yan Najeriya ne suka san inda kansu ke masu ciwo saboda haka babu wani dalilin da wani zai fito daga wata kasa ya basu shawarar yadda zasu tafiyar da harkokinsu. Bisa ga cewarshi, Tony Blair dan kazagin Amurka ne, saboda haka babu wata shawarar kirki da zai ba Najeriya da zai taimaketa.

A nashi bangaren kuma, wani dan gwaggwarmaya, Shehu Sani wanda tun farko ya kushewa gayyatar Tony Blair ya bayyana cewa, Shugaba mai jiran gado Janar Muhammdu Buhari yana bukatar yin taka tsantsan, domin yunkurin da shugabannin da suka gabace shi suka yin a janye tallafin man fetir din bai cimma nasara ba.

Yace Janar Buhari zai janyowa kansa bakin jinni idan ya nemi janye tallafin man fetir din.

Ga ci gaban rahoton.

XS
SM
MD
LG