Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Anyi Hadarin Kwale-Kwale A Bangladash, Ya Kashe Akalla Mutane 37


Kauyawa a Bangladash suke dako kusa da inda aka yi hadarin kwale-kwale a kogin Surma,cikin gundumar Sunamganj.

An yi hadarin kwale kwale a kasar Bangladesh, har ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 37,galibin wadanda hadarin ya rutsa dasu mata ne da yara.

An yi hadarin kwale kwale a kasar Bangladesh,ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 37,galibin wadanda hadarin ya rutsa dasu mata ne da yara.

Hukumomin suka ce galibin fasinjoji maza sun ninkaya zuwa gaba. Jami’ai suka ce a daren jiya Asabar ce kwale-kwalen ya nutse a kogin da ake kira Surma dake arewa maso gabshin kasar,bayan ya yi karo da wani babban jirgin dakon kaya.

Jami’an kasar sukace akalla mutane 80 ne suke cikin jirgin.

Jami’an kasar suka ce jirgin ya nutse ne a gundumar Sunamganj,mai tazarar kilomita 240 daga Dhaka,yana daga cikin yankuna masu nisa,wadda ya yas tsananta kai doki cikin gaggawa.

Bangladash tana da koguna fiyeda 200. Hadarin jirage ya zama ruwan dare kasar saboda rashin dokoki kan masu inganci.

XS
SM
MD
LG