Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya ta Kudu za ta yi Atisaye tare da Harbe-Harbe na Gaske


Wasu sojojin Koriya ta Kudu
Wasu sojojin Koriya ta Kudu

Koriya ta Kudu ta ce za ta sake gudanar da atisaye da harbe-harbe na gaske

Koriya ta Kudu ta ce za ta sake gudanar da atisayen kayan yaki na hakika, a wani tsibiri kusa da gabar Korea ta Arewa, wanda wannan maimaita abin da ya jawo mummunan harin makaman atilaren Koriya ta Arewa ne da ya jawo asarar rayuka a watan jiya.

Jami’an sojin Koriya ta Kudu sun fadi jiya Alhamis cewa atisayen na rana guda da za a yi a tsibirin Yeonpyeong za a yi ne tsakanin ranar Asabar da Talata, bisa ga kyawun yanayi.

Korea ta Arewa ta kai hari kan Yeonpyeong ran 23 ga watan Nuwamba, inda ta kashe ‘yan Korea ta Kudu hudu.

Koriya ta Arewa dai t ace za ta maida martani ga atisayen na Korea ta Kudu wanda zai hada da barin wutar da za a yi da bindigogin atilare daga stibirin zuwa cikin yankin ruwan da bangarorin biyu ke takaddama akai.

Wani babban hafsan sojojin Amurka ya fadi jiya Alhamis cewa Amurka na fargaban yiwuwar a yi dauki ba dadi a mashigin ruwan Koriya idan Koriya ta Arewa ta maida martani ga sabon atisayen Koriya ta Kudun da takala.

Janar James Cartwright, Mataimakin Hafsan Hafsoshin Sojin Amurka, ya ce atisayen da za a yi da harbe-harbe na zahiri za a yi shi ne cikin iyakokin da aka fayyace kuma ta hanya bayyananna, amman ya ce atisayen ka iya jawo martani daga Koriya ta Arewa.

Wannan al’amarin na faruwa ne adaidai lokacin da gwamnan Jahar New Mexico ta Amurka, Bill Richardson, kwararren mai sasanta tsakani kuma tsohon Jakadan Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, ya tafi Koriya ta Arewa a wata balaguro ta radin kansa ta neman kwantar da hankula a mashigar Koriyoyin.

XS
SM
MD
LG