Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bangladesh Zata Gina Sansanin 'Yan Gudun Hijira Mafi Girma a Duniya


Al'umman Muslimin Royhingya dake kokarin shiga ketarewa zuwa kasar Bangladesh
Al'umman Muslimin Royhingya dake kokarin shiga ketarewa zuwa kasar Bangladesh

Sansanin 'yan gudun hijira da Bangladesh zata gina zai samar wa 'yan kabilar Royhigya sama da dubu dari biyar wadanda suke tserewa daga Myanmar inda ake yi masu kisan kiyashi

Kasar Bangladesh za ta gina sansanin ‘yan gudun hijira mafi girma a duniya, wanda zai dauki mutane sama da rabin miliyan ‘yan kabilar Rohingya, wadanda suka tsere daga Myanmar a cewar hukumomi.

‘Yan gudun hijirar wadanda suke warwatse a sansanoni 23 akan iyakar kasar, za su koma wannan babban sansani da ke Cox’s Bazaar, kamar yadda Ministan kula da aukuwar bala’i da ba da agaji, Mofazzal Hossain Chowdhury ya fada a jiya Alhamis.

Ya kuma kara da cewa za a kulle dukkanin sauran sansanonin, idan aka maida su wuri guda, yana mai cewa za su maida hankali ne kan ‘yan gudun hijirar Myanmar.

Kwararar ‘yan gudun hijirar kabilar Rohingya zuwa Bangladesh daga watan Agusta, ya sa adadinsu ya haura sama da dubu 800, tun daga wadanda suka fara shiga kasar daga shekarar 1978.

Sansanin ‘yan gudun hijira mafi girma a duniya shi ne na Bidi-Bidi da ke Uganda, wanda ke dauke da mutanen da aka yi kiyasin za su kai dubu 285.

Wanada ke biye da shi ne sansanin Dadaab da ke Kenya, wanda ke dauke da mutane dubu 245.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG