Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bankin CBN Zai Baiwa Masu Yin Fitan Kayayyaki Daman Samun Bayanai Kan Irin Ribar Da Ake Samu


Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele
Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele

Babban bankin Najeriya wato CBN ya ba wa masu fitan kayayyaki tabbacin cewa zasu cigaba da samun sahihan bayanai kan irin ribar da su ke samu a kan kayayyakin da su ke fitar da su zuwa kasashen waje ba tare da fuskanta matsaloli ba.

Gwamnan babban bankin na Najeriya wato CBN, Godwin Emefiele, ne ya bayyana hakan a yayin gabatar da jawabi a lokacin taron karawa juna sani kan yanayin fitan kayayyaki da bankin Zenith ya shirya wanda aka gudanar ta yanar gizo, inda ya bukaci masu fitar da kayayyakin da su mayar da hannun alkhairi ta hanyar dawowa da kudadden su cikin gida.

A cewar Godwin Emefiele tallafawa cinikayya mafi girma a nahiyar Afrika da sauran kasashen duniya na da mahimmanci ga manufofin babban bankin na Cbn na samar da cigaban tattling arziki da kuma samar da guraben aikin yi ga yawan mutanen Najeriya da ke karuwa yau da kullum.

Haka kuma, Emefiele ya ce, annobar korona birus da tasirin ta kan farashin gangar danyen mai a shekarar 2020, wanda ya yi gagarumin tasiri kan kudadden shigar gwamnatin Najeriya da kudadden shigar ketare ya kara nuna mahimancin karkatar da akalar tattalin arzikin kasar daga dogaro da albarkatun man fetur kadai.

Emefiele ya bayyana kwarin gwiwa kan cewa, yarjejeniyar cinikayyar bai daya maras shinge tsakanin kasashen nahiyar Afirka wato AFCFTA ta ba wa kamfanoni masu zaman kansu na Najeriya damar su fadada kasuwancinsu zuwa sabbin kasuwannin kasashen nahiyar Afrika da kuma neman sabbin hanyoyin fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje, musamman a bangarorin masana'antu, fasahar sadarwa na zamani da bayanai wato ICT, aikin gona da kuma hada-hadar kudi.

Aiwatar da wannan yarjejeniyar cinikayyar bai daya maras shinge tsakanin kasashen nahiyar Afirka wato AFCFTA yadda ya kamata zai ba wa kamafanonin Najeriya daman fitar da kayayyaki da kuma ayyuka da kudinsu zai kai dala biliyan 504 da miliyan 170 zuwa kasuwanni a nahiyar Afrika yana mai ba wa ‘yan kasar shawara da su yi amfani da wannan dama wajen tabattar da cewa, Najeriya ta zama wata babbar cibiyar sarrafa kayayyakin cikin gida da na kasa da kasa da kamafanoni zasu yi ta neman damar a dama da su daga kasuwannin yammaci, tsakiya da ma kudancin nahiyar.

Kazalika, Emefiele ya yi imanin cewa, yarjejeniyar AFCFTA, zata samar wa matasan Najeriya masu basirar kirkire-kirkire fadada ayyukan su zuwa kasashen nahiyar baki daya inda zasu iya samar da dandamalolin kasuwanci da zasu taimaka wajen sayar da kayayyakin da aka sarrafa a kasar ga masu bukata nan takes sauran sassan kasashen nahiyar Afrika ya zama wani bangare na taimaka a fannin samar da guraben aikin yi da zai rage matsalolin zaman kashe wando a kasar tare da bunkasa kudadden shigar ketare.

Daga karshe Emefiele, ya ce bankunan Najeriya sun fara fadada ayyukan su a nahiyar Afrika kamar yadda ya bada umarni ga bankuna su yi amfani da wannan damar kafuwar su wajen tallafawa kasuwancin ‘yan Najeriya da ke neman fadada kasuwancin su zuwa sabbin kasuwanni sauran kasashen nahiyar Afrika ta hanyar ba su rance ga masu karfin bunkasa da biyan bashi.

Idan ba a manta ba, a ranar 7 ga watan Yulin shekarar 2019 ne gwamnatin tarayyar Najeriya ta rattaba hannu a yarjejeniyar cinikayyar bai daya maras shinge tsakanin kasashen nahiyar Afirka wato AFCFTA a birnin Yamai na jamhuriyyar Nijar a yayin taron musamman na kungiyar kasashen tarayyar Afirka wato AU wanda wasu masana tattalin arziki suka yi ta bayyana damuwa kan matakin.

XS
SM
MD
LG