Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Bankin Najeriya Zai Kaddamar Da Kudin Yanar Gizo A Ranar 1 Ga Watan Oktoba


Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele
Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele

Babban bankin Najeriya wato CBN ya bayyana cewa zai kaddamar da kudin yanar gizo da aka dade ana jira, a ranar 1 ga watan Oktobar shekarar nan da mu ke ciki.

Darakta a sashen fasahar bayanai na zamani, Rakiya Mohammed ce ta bayyana hakan a yayin wani taron karawa juna sani da aka gudanar a yanar gizo.

Draktar ta bayyana cewa hukuma mai kula da harkar banki a Najeriya ta fara gudanar da bincike kan fara amfani da kudaden na zamani tun a shekarar 2017.

Malama Rakiya ta kara da cewa akwai yiyuwar babban bankin kasar ya gudanar da aikin kafa hujja na fahimtar yadda kudin zamanin za su sami karbuwa kafin karshen shekarar nan.

Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele ne ya fara yin magana a kan yunkurin fara amfanin da kudin yanar gizo na zamanin ne a yayin taron kwamitin manufofin kudi wato MPC a watan Mayun da ta gabata, yana mai cewa za'a fara amfani da kudin na zamani nan ba da jimawa ba a Najeriya.

Gwamnan na CBN ya kara jadada kudurin bankin na aikin tabbatar da fitar da kudin yanar gizon wato e-Naira a yayin taron kwamitin bankunan kasar karo 306 da za’a yi a cikin kwanan nan.

Rakiya Mohammed ta kuma lissafa alfanun wannan kudi na yanar gizo tana cewa zai taimakawa aikin kula da bunkasa tattalin arzikin kasa, saukaka cinikayyar kan iyakoki, inganta bunkasa hada-hadar kudi da kuma inganta tasirin manufofin kudi.

Haka kuma ta ce wannan tsarin kudin zai taimakawa kudurin daina amfani da kudin takarda, inda ta kara da cewa babban bankin Najeriyar na da kyawawan manufofin kan tsarin don shiga matakin gaba na fara amfani da kudin na zamani.

XS
SM
MD
LG