Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bankin Duniya Zai Ba Najeriya Bashin Dala Miliyan 500 Don Samar Da Wutar Lantarki


Wata tashar wutar lantarki
Wata tashar wutar lantarki

Babban Bankin Duniya ya amince da shirin baiwa Najeriya bashin Dalar Amurka Miliyan 500 domin ta inganta samar da wutar lantarki da kuma fadada hanyoyin sadarwa na kamfanonin rarraba wutar lantarki.

Sanarwar ba da wannan bashi na dauke da sa hannun Darekta Bankin Shubham Chaudhuri wanda aka raba wa manema labarai ta yanar gizo

Darekta Shubham ya ce dalar Amurka Miliya dari biyar zai taimaka wajen bunkasa samar da wutar lantarki ta hanyar inganta ayyukan kamfanonin rarraba wutar wato DISCO's ta hanyar wani gagarumi shirin ma'auni da yan Najeriya ke so tsawo lokaci.

Wani abu da Kwararre a fanin tattalin arziki na kasa da kasa Shuaibu Idris Mikati ya yi nazari cewa wannan irin bashi shi ne ake so kasa ta rika samu domin zai taimaka wajen sayo manyan kayan aiki da za su inganta kasuwancin wutar lantarki ba tare da samun tangarda ba.

Mikati ya kara da cewa Kamfanoni 11 da ke kasuwancin wutar lantarki a kasar ba su da kwarewa wajen tafiyar da su, saboda haka idan ba a samu irin wanan tallafi ba , aikin ba zai tafi daidai ba.

Saboda haka yake kira da babban murya da a sa ido a yadda ake tafiyar da kamfanonin domin a ba yan kasa irin sabis din da ya kamace su.

Sai dai wasu masu fashin baki sun zargi Gwamnati da hada baki da bankin Duniya don a azurta shugabanin kamfanonin.

Mai fashin baki a al'amura yau da kullum Komred Isa Tijjani ya ce bankin duniya za ta ba da kudin ne saboda manya manyan ma'aikatan kamfanonin su samu kudin sharholiya, domin an dade ana zuba zunzurutun kudade a fanin watar lantarki amma ba ta canja zane ba, Isa ya ce wanna yaudara ce kawai ake so a yi wa yan kasa.

Amma Jami'in Kamfanin rarraba wutar lantarki da ke Kaduna Abdulaziz Abdullahi ya ce suna sambarka da samun wanna tallafi, domin sun dade suna kokawa akan rashin kaya aiki da za su taimaka wa kamfanonin wajen yi aiyukan su.

Abdulaziz ya ce ko da yake ba yanzu ne kudin za su shigo hanun su ba amma idan an same su, za a sarrafa su ta hanyar da yan kasa za su amfana.

Bankin Duniya ya ce zai tabbatar da cewa Kamfanonin rarraba wutar lantarki za su zuba hannun jari masu muhimmanci don gyara hanyoyin sadarwa da girka mitocin lantarki da inganta sabis ga wadanda su ka riga suka hada layukan watar lantarkin su.

Saurari cikakken rahoton Medina Dauda Daga Abuja:

Bankin Duniya Zai Ba Najeriya Bashin Dala Miliyan 500 Don Samar Da Wutar Lantarki
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00


XS
SM
MD
LG