Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Banky W. Ya Lashe Zaben Fidda Gwani Karkashin Jam'iyyar PDP A Legas


Banky W (Hoto: Shafin Instagram na Banky W)
Banky W (Hoto: Shafin Instagram na Banky W)

Bayan da aka kammala kidaya kuri’un tare da bayyana sakamakon, masoyan Banky sun dauke shi a kafada suna murnar lashe zaben.

Fitaccen mawakin Najeriya Mr. Olubankole Wellington da aka fi sani da Banky W, ya lashe zaben fidda gwani da aka yi na takarar kujerar dan majalisar wakilai karkashin jam’iyyar PDP a zaben 2023.

Banky ya samu nasara ne bayan da ya samu kuri’u 28 cikin 31 da wakilai suka kada don fitar da wanda jam’iyyar ta PDP za ta tsayar takarar kujerar mazabar Eti-Osa a Majalisar wakilai da ke jihar Legas da ke kudancin Najeriya.

Bayan da aka kammala kidaya kuri’un tare da bayyana sakamakon, masoyan Banky sun dauke shi a kafada suna murnar lashe zaben kamar yadda wani bidiyo da mawakain ya wallafa a Instagram ya nuna.

A shekarar 2019, Banky ya fadi zaben mazabar ta Eti-Osa inda dan takarar APC Babajide Obanikoro ya kada shi.

A badi ne za a gudanar da zaben gama gari a Najeriyar ciki har da na ‘yan majalisar wakilai.

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG