Accessibility links

Barayi su kashe kimamin mutane ashirin da uku a Zamfara

  • Jummai Ali

Wasu wadanda ake zaton yan fashi da makami ne sun kashe mutane ashirin da uku a karamar hukumar Malu ta jihar Zamfara.

Wasu 'yan fashi da makami sun kashe mutane ashirin da uku a gundumar Dansadau, a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara. Haka kuma an raunana wasu da dama.

Wakilin sashen Hausa Murtala Faruk Sanyinna ya aiko da rahoton cewa ana kyautata zaton yan fashin sun yi kisan ramuwar gaiyace a saboda kashe takwarorin aikinsu barayi da aka yi a yanki.

Wannan ne karo na uku da aka kai harin ramuwar gaiya a cikin shekara guda a jihar Zamfara, kamar yadda za'a yi karin bayani a wannan rahoto.

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG