Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Barcelona Ba Ta Bukatar Suarez


Luis Suarez

Kungiyar kwallon kafar Barcelona ta kasar Spain ta ce ba ta da sauran bukatar shahararren dan wasanta Luis Suarez.

Suarez na da sauran shekara daya da ta rage a kwantaraginsa da Barcelona, to amma ta yiwu ya bar kungiyar a wannan bazarar.

Rahotanni sun bayyana cewa sabon kocin kungiyar Ronald Koeman, ya fadawa dan wasan dan kasar Uruguay da ya kama gabansa, domin ko bai da bukata da shi a kungiyar.

Luis Suarez
Luis Suarez

Suarez ya kafa tarihin kasancewa dan wasa na 3 da ya zurawa kungiyar ta Barcelona kwallaye mafi yawa a tarihi da kwallaye 198 da ya zura mata.

Dan wasan mai shekaru 33, yana karbar albashin fam 290,000 a kowane mako a kungiyar, to amma daya daga cikin ayukan da aka dorawa sabon koci Koeman, shi ne rage yawan kudaden da ake biyan ‘yan wasa a kungiyar.

Ronald Koeman, Sabon Kocin Barcelona
Ronald Koeman, Sabon Kocin Barcelona

A makon da ya gabata ne Suarez ya nemi kungiyar da ta bayyana masa matsayin zamansa, bayan ta ba da sanarwar saka kusan dukkan ‘yan wasanta a kasuwa.

Facebook Forum

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG