Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Barcelona Na Dab Da Rasa Messi


Lionel Messi
Lionel Messi

Barcelona na dab da rasa kambinta na gasar La Liga, to amma babbar matsalar da za ta fi haka muni shi ne rasa gwarzon dan wasanta Lionel Messi.

Kwantaragin Messi zai karkare a kungiyar ne a shekara mai zuwa, a yayin da kuma rahotanni su ka ce ya daina maganar sabuntawa da kowa, sakamakon takaicin yadda alkiblar kungiyar ke tafiya.

Wani gidan rediyon kasar Spain mai suna Cadena Ser, ya ruwaito cewa “Messi na shirin barin kungiyar ta Barcelona,” inda ta ce “yanzu haka dan wasan na jiran karewar wa’adin kwantaraginsa ne kawai.”

A watan Fabrarirun da ya gabata Messi ya bayyana cewa ba ya tunanin Barcelona za ta iya lashe gasar zakarun Turai da irin yanayin da take ciki.

Haka kuma dan wasan mai shekaru 33, ya yi ta samun takun saka da rashin jituwa da shugabannin kungiyar, a karkashin jagorancin Joseph Maria Bartomeu.

Abubuwan Bajinta Biyar Da Har Yanzu Lionel Messi Ke Zarra Kai
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:40 0:00

Facebook Forum

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG