Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Batun Boko Haram Ya Mamaye Taron Yaki Da Ta’addanci Na Jami’ar California


Shugaban ‘yan kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau, Oktocba 2, 2014.
Shugaban ‘yan kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau, Oktocba 2, 2014.

Batun ta’addancin Boko Haram a Najeriya shine ya mamaye taron da aka gudanar a jami’ar California, kan yaki da ta’addanci da ‘yan jaridu daga kasashen duniya suka halarta.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka, ta gayyato ‘yan jaridu daga sassa daban-daban na duniya, inda yanzu haka suke samun horo tare da rangadin jihohi daban-daban da jami’o’i da ma cibiyoyi na ‘kasa da ‘kasa a nan Amurka.

Batun tarzomar Boko Haram ce ta mamaye taron na jami’ar California, Farfesa Brandi Bangle, dake zama mataimakin daraktan sashen kimiyyar siyasar duniya a Jami’ar da kuma yayi tsokaci kan Boko Haram, ya ce ‘daya daga cikin abin da ya kamata ai la’akari dashi shine idan ana batun ta’addanci irin na Boko Haram, to Akida ce ke musu jagoranci.

Saboda haka ba za a maida hankali wajen amfani da karfin soji kadai ba, amma ya kuma kyautu a maida hankali wajen yaki da ainihin akidar dake haddasa wannan tsatauran ra’ayi. Ya ce wasu daga cikin mayakan Boko Haram din na cikin kungiyar ne bisa tursasawa yayin da wasu kuma basu san ainihin abin da yasa suke ciki ba.

Farfesa Brandi wanda ya yabawa kokarin gwamnatin Najeriya bisa nuna da gaske take wajen yakar Boko Haram, amma yayi gargadin amfani da karfin soji kadai ba zai kawo karshen matsalar ba a gaba daya, don haka akwai bukatar daukan karin wasu matakai.

Wakilin Muryar Amurka Hassan maina kaina, dake cikin tawagar ‘yan jaridun, ya tambayi daraktan sashen bincike mai zurfi kan ta’addanci na jami’ar ta california Farfesa Ashko Potato, tun farko ma meke haddasa ta’addancin? inda ya ce akwai dalilai da dama amma babban dalili shine akida na da ga bin da akai imani dashi na haddasa bijirewa.

Ya ce suna bincike akan abin da yasa mutane ke bijirewa bayan kuma a baya ana zaman lafiya dasu cikin al’umma, koda yake basu fara zurfafa bincike kan Boko Haram a Najeriya ba, saboda ba a gayyace suba.

Don karin bayani ga rahotan Hassan Maina Kaina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG