Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Batun Bukatar Ciwo Bashi Ya Raba Kawunan 'Yan Majalisar Wakilai


ABUJA: Sanata Ahmed Babba Kaita

Bukatar ta shugaban kasa ta neman ciwo bashi daga ketare na dalar Amurka biliyan talatin ya raba kawunan 'yan majalisar wakilan kasar.

Wasu suna goyon bashin amma wasu kuma suna ganin ba lokacin ciwo bashi ba ne tunda ba'a riga an kashe kasafin kudin bana ba.

Ahmed Babba Kaita ya bayyana ra'ayinsa. Yace gwamnatocin da suka shude sun ki saka hannun jari a ayyukan da zasu dinga kawo kudin shiga sai aka dogara ga mai kawai. Shi bashin za'a gina abubuwan da zasu kawo kudin shiga domin tattalin arziki ya farfado.

Dan Majalisa Muhammad Umar Bago yace shi bai goyi bayan karbo bashi ba. Yace ciwo bashin tamkar an koma baya ne. Yace kasar ta wahala akan basussuka da kyar ta fito daga kangin bashi. Yace duniya gaba daya tana cikin tabarbarewar tattalin arziki. Kamata yayi a hakura domin zai wuce.

Dan Majalisa Muhammad Usman Bago
Dan Majalisa Muhammad Usman Bago

Najeriya ta dogara ne kacokan kan kudin man fetur. Amma kasuwar man ta fadi.Onarebul Aminu Shehu Shagari yace shi ba zai ki ko ya yadda ba sai an gaya masa wasu abubuwa. Yana son ya san ka'idojin bashin da ruwan dake kai, kuma shekaru nawa za'a yi ana biyan bashin. Shin za'a kashesu akan abubuwan da zasu kawo kudaden shiga.

Dan Majlisa Muhammad Usman Bago
Dan Majlisa Muhammad Usman Bago

Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:54 0:00

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG