Accessibility links

Batun Zaben Shugabannin Majalisun Tarayyar Najeriya Yana Da Sarkakiya-Dr Bako

  • Grace Alheri Abdu

Nigeria National Assembly

Akwai matsalar gaske a batun majalisar Tarayyar Najeriya ta fannoni biyu, idan aka dubi lamarin ta fannin ilimin kimayyar siyasa, ko kuma tsarin mulkin kasa, wanda yake kawo saiko a cimma masalaha dangane da zaben shiugabannin Majalisar Tarayyar Najeriya

Dr Abbati Bako na Cibiyar Damokaradiya ta kasa da kasa yace akwai matsalar gaske a batun majalisar Tarayyar Najeriya ta fannoni biyu. Yace idan aka dubi lamarin ta fannin ilimin kimayyar siyasa, za a ga cewa, a ka’idojin damokaradiya kusan guda arba’in, sun kunshi cewa, majalisu su zabi shugabanninsu da suke so. Sai dai a daya bangaren kuma, ana bukatar tambaya kan ko jam’iya tana da hurunin nunawa ‘ya’yanta abinda take so.

Dr Bako yace, tsarin mulkin Najeriya shine muhimmi,, shine kan gaba a kan kowacce doka. Saboda haka ya bada dama abi abinda jam’iya tace, tunda yake mutum baya tsayawa takara , ta kai da halinka sai ya jingina da jam’iya.

Sai dai kuma Dr Bako yace, ana bukatar a kula da cewa, suma ‘ya’yan jam’iyar suna da ‘yancin su zabi wanda suke so ba tare da tsamgwama ko kuma an yi masu katsalandan ba. Saboda haka, yace, matsalar a nan ita ce, yaya za a rabe wanda yafi gaskiya? Jam’iya wadda ta kekasa kasa tace ita zata bada umarni kan wadanda take so a ba shugabanci, ko kuma ‘yan majalisa da suka ce haka ba zata sabu ba?

Ga cikakkiyar hirar da Ladan Ibrahim Ayawa ya yi da Dr Abati Bako .

XS
SM
MD
LG