Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bauchi-Wakilan Jihohin Borno Da Zamfara A Musabakar Alkur'ani Ta Kasa Sun Yi Fice A Bangaren Maza Da Mata


Gwamnan Bauchi Bala Mohammed (Kauran Bauchi)

An kammala gasar musabakar karatun Alku'ani ta kasa kashi na 36 da aka kwashe kwanaki tara ana gudanarwa a jihar Bauchi, inda jihar Borno ta zo ta daya a fannin maza, a yayin da kuma a bangaren mata jihar Zamfara ta zo ta farko.

A jawabinsa na bayyana godiya game da yadda musabakar ta gudana, Gwamnan Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Muhammed Kauran Bauchi, ya ce kwanaki tara da aka yi ana fafatawa a musabakar tsakanin matasa maza da mata, daga jihohi 36 da kuma Abuja, kowanne ya nuna kokarinsa a fannin da ya yi takarar akai,

Gwamnan na Bauchi ya yabawa alkalai da suka yi alakalanci a musabakar, kuma ya ce sun gudanar da hukunci da ya dace wanda kowa ya yi na’am da shi kana aka yaba da shi.

A jawabinsa na rufe musabakar, Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar, shima ya yabawa Gwamnan jihar Bauchi da uwargidansa sabili da daukar nauyin gudanar da musabakar inda ya yi addu’ar Allah Ya saka da Aljannatul Firdaus.

An dai fara gudanar da musabakar karatun Alkur’ani a Najeriya a shekarar 1986 a karkashin jami’ar Usman Danfodio dake Sakkwato. Wadanda zasu zo na farko a bangaren maza da mata sune zasu wakilci kasar Najeriya a musabakar duniya da za a gudanar a kasar Saudi Arabiya.

Ga rahoton Abdulwahab Mohammed cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00

Shugaban Azman

Dalilin Da Yasa Muka Dakatar Da Tafiya Yajin Aikin Sufurin Jiragen Sama a Najeriya - Shugaban Azman
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:17 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Sojojin Najeriya sun samu nasarar kwace bindigogi sama da 500

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Shugaban NDLEA a Najeriya, Janar Buba Marwa

Dalilin Da Ya Sa Muke Bin Diddigin Dukiyar DCP Abba Kyari - Buba Marwa
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:19 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Gwamna Matawalle

Dalilan Da Suka Sa Muka Sayi Motoci Ga Sarakuna A Zamfara - Gwamna Matawalle
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:35 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG