Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Ya Yabawa Darakta Janar din NIPPS Na Farko


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Shugaba Muhammad Buhari ya yaba wa darakta janar na farko na NIPSS dake Jos, Manjo Janar Timothy Babatunde Ogundeko wanda Allah ya yiwa rasuwa.

Shugaba Buhari ya bayyana marigayin a matsayin wani gwarzo wanda ya kasance a kan gaba wajen bada misali a dabarun koyas da tsarin shugabanci.

Yayinda za'a binne gawar Janar Ogundeko a karshen wannan makon, Shugaba Buhari ya tabbata za'a dade ana tunawa da marigayin saboda rawar da ya taka a matsayin jan gwqarzo mai ilimantarwa da kasancewa wanda ya kware a gudanar da harkokin jama'a.

Janar Ogundeko ya kawo gudummawa wajen hanyoyin horas da shugabannin tsaro domin inganta tsaro da harkokin siyasar Najeriya.

Shugaba Buhari ya jaddada cewa, nacewarsa da yin kokari tare da hangen nesa suka sa Janar Ogundeko ya kawowa cibiyar koyas da sojoji canjin da ya dace da ya kawowa kasar anfani. Shi ne kuma ya yi tsayin dakar ganin an kafa makarantun sakandare na sojoji da suka samu karbuwa mai kyau.

Shugaba Buhari yace yayi imani manufar marigayin na tabbatar da Najeriya ta zama tsintsinya madaurinkin daya da kasancewa kasa mai albarka, masu juyayinsa zasu mutuntata saboda girmamashi. Yin hakan ya zama wajibi musamman a lokacin da kasar take bukatar 'yan kasar da suka sadakar da kansu domin a canza Najeriya ta zama kasa mai kyau fiye da da can.

Shugaban ya mika ta'aziyarsa wa iyalan Janar Ogundeko da kuma gwamnati da duk ilahirin al'ummar jihar Ogun, jihar marigayin.

Yayi addu'ar Allah ya sa marigayin ya huta da fatan ya karfafa iyalansa da a'yanuwa da abokansa

XS
SM
MD
LG