Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bayan Shekaru Talatin Yanzu An Soma Dakon Shanu da Jirgin Kasa daga Arewacin Najeriya zuwa Kudanci


Shanu da yanzu an soma sufurinsu da jirgin kasa zuwa kudu daga arewan Najeriya
Shanu da yanzu an soma sufurinsu da jirgin kasa zuwa kudu daga arewan Najeriya

Yau sama da shekaru 30 kenan rabon da aga ana safaran kayayyakin masarufi cikin jirgi daga kowanne sashe na Najeriya.

Amma cikin wannan satin sai ga jirgin kasa ya tashi daga birnin Gusau fadar Gwamnatin jihar Zamfara dauke da shanu ya dunfari birnin Ikko.

Sau tari dai a Najeriya sun fi mayar da hankali ne da tafiya a cikin motocin bas-bas ko kuma daukar kaya da manyan motoci wanda sau tari suna karo da matsaloli da yawa.

Kama daga rashin kyawon hanya zuwa karancin man fetur sai kuma fashi da makami da rashin tsaro .

Ana iya cewa daukar dabbobi daga Gusau zuwa birnin Ikko wani hubbasa ne da zai taimaka gaya ba a harkokin sufuri kawai ba a’a harma da rage tsananin rayuwa, ta fannoni daban-daban.

Haka kuma yawan dogaro da anfani da hanya shima zai ragu, kuma zai taimakawa harkokin kasuwancin dabbobin kamar yadda Alhaji Bello Dan Mubaffa sarkin Fulanin kasuwan shanun yace.

Jirgin kasa dai ya gitta sassa daban-daban na Najeriya kuma turawan mulkin mallaka ne suka gina shi tun a shekarar 1960.Sai dai ko can da mutanen Najeriya sunfi dogaro da hanyar mota wajen gudanar da harkokin su na sufuri.

A lokutta da dama Najeriya tasha kokarin farfado da hanyar dogo, musali a shekarar 2012 anyi wannan yunkurin daga Lagos zuwa Kano amma lamarin bai dore ba.

Kawo dabbobi musammam shanu daga arewacin Najeriya zuwa kudanci musammam Lagos cikin jirgin kasa zai taimaka dabbobin isowa cikin koshin lafiya, kana hakan zai rage yawan fadan da ake samu tsakanin makiyaya da manoma.

Haka kuma yanzu kudin dauko dabbobin zai ragu wanda hakan yana nufin raguwar kudin da za a sayar dasu.

XS
SM
MD
LG