Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bayani akan Na'urar Tantance Katin Zabe


Na’urar Card Reader na tantance masu kada kuri’a da zarar an sa hotun su ko kuma yatsunsu. Na’urar dai a zaben shekarar nan ta 2015 ne hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta ta fara amfani da ita.

Wasu masu jefa kuri’a sun bayyana gamsuwarsu da na’urar tantance masu zabe bayan da aka tantancesu, inda suka ce na’urar tayi aiki ba tare da bata lokaci ba. Amma shi kuma Mr. Chinedu Nwora bai taki sa’a ba don kuwa na’urar sai ta bashe shi.

Shugaban masu sa ido na kungiyar tawagar kasashen Turai da ake kira EU a takaice Mr. Santiago Isela Fisas ya fadi cewa na’urar tayi aiki a wasu rumfunan amma a wasu wuraren kuma sai aka sami akasin haka. Buga da kari na’urar ta bata lokaci a wuraren da aka sami turjiya.

Sai da babu laifi a zaben na bana ganin yadda ‘yan Najeriya suka zaku da zaben da kuma yadda suka fito kwansu da kwarkwatarsu don kada kuri’a, a cewar Mr. Isela.

Ga karin bayani a cikn sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:50 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG