Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bayern Munich Ta Ce Wakilan Wasu Jaridun Ingila Ba Zasu Shiga Filinta Ba - 4/4/2014


Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta ce ba zata bayarda takardun iznin halartar karo na biyu na gasar cin kofin zakarun kulob kulob na Turai da zata yi da Manchester United a Jamus ga wakilan wasu jaridu biyu na Ingila ba, a saboda kanun labarai da suka buga na batunci ga dan wasanta Bastian Schweinsteiger.

A bayan da aka ba dan wasan na Bayern jan kati aka kore shi daga fili a kunnen dokin da suka yi da Manchester United, Jaridun The Sun da The Daily Mirror, sun buga kanun labarai dake kiransa da wani suna mai kama da sunansa, amma kuma a Jamusanci yana nufin alade.

Kungiyar Bayern ta yi tur da wadannan jaridun a saboda abinda ta kira "rashin mutunci da wariya da kuma nuna kyamar" da suka yi ma dan wasan nata, ta kuma tabbatar da cewa ba zata ba wakilan wadannan jaridun iznin shiga filin wasa na Allianz Arena domin karo na biyun da za a yi a mako mai zuwa ba.
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:00 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG