Kungiyar kwallon kafar Bayern Munich ta kasar Jamus ta ragargaza Barcelona da zunzurutun ci 8-2, a wasan quarter-final ta gasar zakarun Turai a Lisbon a ranar Juma’a, kashi mafi muni da kungiyar ta sha a tarihi.
Thomas Mueller ya zura kwallaye 2 tare da kwallayen da Ivan Perisic da Serge Gnabry suka jefa a cikin muntuna 31 da soma wasan, wadanda a cikinsu kuma dan wasan Bayern din David Alaba ya sha kansu bisa kuskure.
Luis Suarez ya zurawa Barcelonar kwallon ta 2 da dawowa hutun rabin lokaci, wanda ya kara kuzarin ‘yan wasan kungiyar da ke son farke kwallayen 4-2, to amma kuma Bayern din ta kara fusata ta kuma zura wasu kwallayen 4 ta hanyar ‘yan wasanta Joshua Kimmich, Robert Lewandowski da Philippe Coutinho da ya shigo wasan daga baya.
Coutinho dan wasan Barcelona ne da ke zaman aro a Bayern. Barcelona ta kashe makudan kudade wajen sayen dan wasan dan kasar Brazil a shekara ta 2018.
Wannan ne nasara ta 19 a jere a da Bayern din ta yi a wasannin gasar ta zakarun Turai, kuma ita ce wasa ta 28 da ta buga ba tare da an doke ta ba a gasar, inda kuma yanzu haka ta ke da kwallaye 39 da ta zura a gasar a wannan kakar wasannin.
Facebook Forum