Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Belgium Ta Ba Laurent Gbagbo Mafaka

Tsohon shugaban Ivory Coast Laurent Gbagbo a kotun ICC da ke Hague a kasar Netherlands, ranar 15 ga watan Janairu, 2019.

Kakakin kasar Belgium, Karl Lagatie, ya ce gwamnatinsu, ta ba Gbagbo mafaka ne saboda hakan na daya daga cikin irin gudunmuwar da suke ba kotun ta hukunta manyan laifuka ta ICC domin ta yi nasara a ayyukanta.

Kasar Belgium ta amince ta bai wa tsohon shugaban kasar Ivory Coast, Laurent Gbagbo mafaka, bayan da kotun hukunta manyan laifuka ta ICC ta wanke shi daga tuhumar da ake masa, lamarin da ya zo wa mutane a ba-zata.

Kotun ta ICC ta saki Gbagbo bayan gindaya masa wasu sharudda, inda aka ce ya zauna a kasar da ta ba shi mafaka, sannan kada ya tuntubi wani shaida daga cikin mutanen da ke da hannu a wannan shari’a, ko kuma ya yi magana a baina jama’a dangane da abin da ya shafi shari’ar.

Kakakin kasar Belgium, Karl Lagatie, ya ce gwamnatinsu, ta ba Gbagbo mafaka ne saboda hakan na daya daga cikin irin gudunmuwar da suke ba kotun ta hukunta manyan laifuka ta ICC domin ta yi nasara a ayyukanta.

A ranar 15 ga watan Janairu aka wanke Gbagbo da Charlse Ble Goude da ake tuhumarsu tare, kan aikata ayyukan cin zarafin bil Adama, inda a lokacin, kotun ta ICC ta ki sakinsu har sai sun sami kasar da za ta ba su mafaka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG