Kungiyar kwallon kafar Benfica ta kasar Portugal ta tsawaita aikin sabon mai horar da ‘yan wasanta na rikon kwarya Nelson Verissimo.
Verissimo zai shugabanci kungiyar har ya zuwa kammala sauran wasanni hudu da suka rage na gasar league, bayan da ya maye gurbin koci Bruno Lage a karshen mako.
Kungiyar wadda yanzu haka ke rike da kofin gasar league ta kasar, ita ce ke jagorancin teburin gasar kafin dage buga wasanni a sakamakon annobar coronavirus.
To sai dai shugabancin ya kubuce mata bayan dawowa buga wasanni, sakamakon kashi da ta sha a wasanni biyu, ta kuma yi kunnen doki biyu a cikin wasanni 5 da aka buga bayan dawowa, lamarin da ya sa kungiyar FC Porto ta haye samanta da tazarar maki 6.
Hakan kuma ya sa kocin kungiyar Lage yin murabus a makon da ya gabata, a yayin da Verissimo mai shekaru 43 da a da shi ne mataimakin koci, ya karbi aikin a matsayin rikon kwarya a karshen mako, inda ya jagoranci kungiyar a wasan da ta yi nasarar doke Boavista da ci 3-1.
Facebook Forum