Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Benny Gantz Ya Soke Ganawa Da Benjamin Netanyahu


Netanyahu da Gantz

Tsohon shugaban rundunar sojin Isra’ila, Benny Gantz, ya soke wata ganawa da aka shirya za su yi da Firai Ministan kasar Benjamin Netanyahu a yau Laraba.

Wannan mataki, wani koma-baya ne ga yunkurin da ake yi na kafa gwamnatin hadaka.

Gantza ya ce dalilin soke ganawar shin ne ba a cika sharurddan da aka gindaya kafin a yi zaman ba, amma ya ce mai yiwuwa nan gaba a cikin makon nan a sake saka wata rana da za a gana.

Jam’iyyar Likud ta Netanyahu, ta ce ta “kadu” matuka da ta ji matakin da Gantz ya dauka na soke zaman tattaunawar.

Jam’iyyar ta kuma yi kira a gare shi, da ya sake zurfin tunani domin a kaucewa sake yin wani zabe.

Zaben kasar na Isra’ila da aka kammala a kwanan nan, shi ne na biyu da aka gudanar cikin wannan shekara, wanda shi ma ya gaza samar da wata jam’iyyar da ta samu nasarar da za ta kafa gwamnati ita kadai.

Shugaban kasar ta Isra’ila Reuven Rivlin ne, ya nemi Netanyahu da ya yi kokarin kafa gwamnatin hadaka, amma Gantz ya ce ba zai hada gwamnati da Netanyahu da ake zargi da laifin rashawa ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG