Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Mutum 35 Tare Da Kone Kauyensu a Benue


A kalla mutum 35 ne aka kashe wasu dayawa kuma suka bace a wani harin da ‘yan bindiga suka kai kauyen Tse Umenger dake karamar hukumar Guma a jihar Benue.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan da suka kai kimanin 50 sun afkawa kauyen Tse Umenger ne da missalin karfe bakwai na yammacin ranar Talata.

Inda suka kashe mutum 35 suka kuma cinnawa daukacin gidajen kauyen wuta, yayin da wasu da ba a san adadinsu ba har yanzu ba a san inda suke ba. har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto hukumomi basu ce komai kan batun ba.

Daga jihar Nasarawa dake makwabtaka da Benue wani sabon rikici ya barke tsakanin kabilun Bassa Ibra a wasu yankunan karamar hukumar Toto, lamarin da ya kai ga rasa rayuka.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa Idris Kennady ya tabbatar da cewa an kone gidaje da motoci da babura, haka kuma an kama mutum biyu tare da karbe wasu bindigogi guda bakwai.

Alhaji Attahiru dake zama shugaban al’umma a yankin Toto, ya tabbatarwa da Muryar Amurka mutuwar mutum biyar a rikicin na Ibbra da Bassa, haka kuma yayi kira ga gwamnatocin tarayya da jiha da su duba batun satar mutane da ake yi kusan kullum a yankin.

Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Zainab Babaji.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG