Fafutukar neman tsayawa takarar shugaban kasar Amurka na jam’iyyar Democrat na kara raguwa daga ‘yan takara fiye da 20 ya zuwa tsakanin ‘yan takara 2, bayan gagarumar nasarar da Tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden da dan majalisar dattawa daga jihar Vermont Sanata Bernie Sanders suka samu a zabukan jiya Talata.
Biden ya lashe zabe a jihohi 9, ciki har da jihar Texas mai wakilan dake zaben fitar da gwani (wato delegates) masu yawan gaske, inda nasarar da ya samu ta zo da mamaki, bayan da kuri’un ra’ayoyin jama’a a can farko suka nuna cewa Sanders ne ke da rinjaye mai karfin gaske a yankin.
Haka kuma ya sami nasarar lashe yankin kudancin Amurka, inda ya yi galaba a jihohin Virginia, North Carolina, Alabama, Oklahoma, Tennessee da Arkansas, hadi da Minnesota da Massachusetts.
To sai dai shi ma Sanders ya sami wasu jihohi da suka fi yawan delegates, wato California, Colorado Utah, da kuma jiharsa ta Vermont.
Za ku iya son wannan ma
-
Fabrairu 23, 2021
Jirgin Hukumar Sama Jannatin Amurka Ya Isa Tashar Sararin Sama
-
Fabrairu 22, 2021
COVID-19 :Adadin Wadanda Suka Mutu Ya Kusa Rabin Miliyan A Amurka
-
Fabrairu 20, 2021
Amurka Ta sake Komawa Cikin Yarjejeniyar Sauyin Yanayi A Hukumance
-
Fabrairu 17, 2021
Texas-Dussar Kankara Ta Haifar Da Dauke Wuta A Gabashin Amurka