Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bikin Kasa Na 16 Na Sarafa Kaya A Najeriya


Mukaddashin Shugaban Najeriya Farfasa Yemi Osinbajo yayinda yake jawabi a bikin

Yau shekaru goma sha shida ke nan da Najeriya take bikin sarafa kaya a kasar tare da bada lambobin yabo ga wadanda suka yi fice da zummar harzuka mutane su zabura su dinga sarafa kaya walau na abinci ko na sawa da makamantansu

Yau mukaddashin shugaban Najeriya Farfasa Yemi Osinbajo ya kaddamar da bikin sarafa kaya na goma sha shida a birnin tarayyar kasar tare da bada lambobin yabo ga wadanda suka yi fice a shekarar da ta gabata.

Shi wannan bikin an fara shi ne shekaru goma sha shida da suka gabata da zummar karfafa 'yan kasar su tashi tsaye wajen sarafa kaya walau na abinci ko na sawa ko na yin wasu ayyuka da dai sauransu domin inganta tattalin arzikin kasa.

Wadanda suka kasance a wurin taron sun hada da ministar kasuwanci da saka jari Hajiya Aisha Abubakar da Muhammad Bello, ministan birnin tarayya da Dr. Chris Ngige ministan kwadago da samar da aiki da Dr. Kayode Fayemi ministan ma'adanai da kuma ministan yada labarai Alhaji Lai Muhammad.

Bikin ranar sarafa kayan abinci; Aisha Abubakar ministar kasuwanci, Muhammad Bello ministan birnin tarayya. Mukaddashin shugaban kasa Farfasa Osinbajo,Chris Ngige ministan kwadago, Kayode Fayemi ministan ma'adanai da Lai Muhammad ministan labarai
Bikin ranar sarafa kayan abinci; Aisha Abubakar ministar kasuwanci, Muhammad Bello ministan birnin tarayya. Mukaddashin shugaban kasa Farfasa Osinbajo,Chris Ngige ministan kwadago, Kayode Fayemi ministan ma'adanai da Lai Muhammad ministan labarai

A wurin bikin Mukaddashin Shugaban Kasa Farfasa Yemi Osinbajo ya raba lambobin yabo ga wadanda suka yi fice a shekarar da ta gabata. Dr. Yemi Kale babban daraktan hukumar kidigdiga na kasar ya samu lambar yabo mafi girma.

Wannan bikin dai an gudanar dashi ne a katafaren otel din nan dake Abuja da ake kira Nicon Luxury Hotel.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG