Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihar Borno Na Samarwa Da Matasa Aikin Yi Don Yakar Ta’addanci


Yayin da rikicin Boko Haram ya fara lafawa a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, jihohin da lamarin ya shafa na kokarin farfadowa ta hanyar samarwa matasa ayyukan yi.

A wata tattauna da babban editan sashen Hausa na Muryar Amurka yayi da gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya bayyana wasu hanyoyin da yayi amfani da su wajen yakar ta’addanci a jiharsa.

Shettima yace idan har ana son yakar ta’addanci dole ne a samarwa da matasa aikin yi, musamman ta fanni Noma da gine-gine. Kasancewar idan har matasa na da aikin yi tabbas fituna za ta yi ‘kasa.

Ya ci gaba da cewa idan har shugabanni na son zaman lafiya a Arewa, ya zama dole su tashi tsayin daka domin ceto al’ummarsu. Idan ba haka ba nan da shekaru goma zama ka iya yi musu wahala yankin.

Jihar Borno itace jihar da Boko Haram ta fi yiwa illa a yan shekarun baya, amma bincike ya nuna cewa tana daya daga cikin jihohin da ma’aikata basa binta bashin albashi, maimakon hakan har ‘karawa ma’aikatan jihar kudi akayi.

Domin karin bayani saurari hira ta musamman da gwamnan jihar Borno Kashim Shettima.

please wait

No media source currently available

0:00 0:16:49 0:00

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG