Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bikin Murnar Shiga Sabuwar Shekara a Legas


An gudanar da bukukuwan murnar sabuwar shekara a birnin Legas, inda dubban mutane suka hallara a Majami’u da wasu cibiyoyin raye-raye da wake-wake domin murnar shiga sabuwar shekarar 2018.

Wakilin Muryar Amurka ya zaga a birnin Legas inda ya tattauna da wasu ‘yan Najeriya, wadanda suka bayyana fatansu na samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar cikin wannan sabuwar shekara da aka shiga.

Da yawa daga cikin ‘yan Najeriya sun yi kira ne ga hukumomi da su kara azama wajen inganta jin dadin al’ummar kasar da samar da wutar lantarki da tsaro da kuma kawar da talauci.

An dai gudanar da addu’o’i a Majami’u daban-daban a birnin Legas, a jajiberan shiga sabuwar shekara domin godiya ga Allah da fatan nasara a sabuwar shekarar da aka shiga.

Domin karin bayani ga rahotan Babangida Jibrin daga Legas.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:01 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG