Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Billy Graham Ya Rasu Ya Na Da Shekaru 99


Mai Bishara Billy Graham
Mai Bishara Billy Graham

Allah ya yiwa fitaccen mai bishara Billy Graham rasuwa ya na da shekaru 99 da haihuwa a duniya a gidansa dake Montreat cikin jihar Carolina ta Arewa

Fitaccen mai bishara Ba’amurke Billy Graham da ake dauka a matsayin wanda yafi kowanne mai wa’azin addinin Kirista tasiri a karni na ishirin ya rasu yau yana da shekaru casa’in da tara.

Graham ya yi fama da rashin lafiya cikin shekarun da suka gabata, ya kuma rasu a gidanshi dake Montreat jihar Carolina ta Arewa. Ya jima baya fita a bainin jama’a ko da yake ya halarci bukin cika shekarunsa casa’in da biyar a watan Nuwamba shekara ta dubu biyu da goma sha uku.

Graham ya shafe shekara da shekaru yana daga Littafi Mai Tsarki sama yayinda yake wa’azi ga sama da mutane miliyan dari biyu a kasashe dari da tamanin da biyar na duniya. Ya shirya manyan tarukan bishara da ake kira Billy Graham Crusades da dubban mutane suka halarta, ya kuma yi wa’azi ga miliyoyin mutane ta akwatin talabijin da radio da kuma tauraron dan adam. A cikin shekaru saba’in da Billy Graham ya shafe yana bishara, ya fayyace cewa, bangaskiya da kuma karbar Yesu Almasihu itace kadai mafita ga masifun da bil’adama ke fuskanta.

Billy Graham ya yi wa’azi a kowacce nahiya ta duniya sai dai Antarctica kadai. Yayi wa’azi a kasashen tarayyar Soviet kafin rugujewar kwaminisanci, yayi wa’azi a China da Koriya ta arewa inda ya gana da shugabannin siyasar kasashen.

Mai bisharar ya zama mashawarcin al’amuran ruhaniya ya kuma shaku da dukan shuganannin Amurka daga Harry Truman a shekara ta dubu da dari tara da arba’in zuwa Barack Obama a karni na ishirin da daya. An sha gayyatar Billy Graham ya yi addu’a a manyan taruka da kuma bukukuwa na kasa a Amurka, da suka hada da rantsar da sabbin shugabanni.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG