Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bincike Akan Sama Da Fadi Kan Kudi Sama Da Biliyan Goma A Jihar Jigawa


Cikin wadanda majalisar dokokin jihar Jigawa ke tuhuma sun hada da wasu tsofaffin kwamishinoni da shugabannin kananan hukumomi da kuma wasu ma’aikatan gwamnati da majalisar dokokin jihar take zargin sun fitar da wasu kudi fiye da Naira Bilyan goma, wadanda kodai an fitar dasu daga lalitar kananan hukumomi ba ta hanyar data dace ba ko kuma an salwantar da su ta hanyar da bata dace ba.

Honorable Idris Garba Jahum, shugaban majalisar ta Jigawa ya ce kudin da ake bincika a yanzu daga shekara ta 2008 ne shekara ta 2015, kuma kudi ne da aka riga aka tantance daga majalisa akan kasafin kudin da za’a kasha, kuma an riga an zayyana yadda za’a kashe wadannan kudi.

Shugana ya kara da cewa an cire kudin, kuma dalilin daya sa suke kokarin binciken domin ganin shin an fitar da kudin a ka’idance kokuwa?, sa’an nan da aka cire kudin mai aka yi da su?.

Wasu daga cikin kwamishinonin da suka rike ma’aikatar kananan hukumomi a jihar a zamanin tsohuwar gwamnatin suka bayyana a gaban majalisar dokokin dake gudanar da wannan bincike, amma Alhaji Jahum, dake zaman shugana jam’iyyar PDP a shiyyar Jigawa ta tsakiya, ya ce aikin binciken siyasa ce kawai.

Yanzu haka dai talakawan jihar ta Jigawa sun fara tsokaci akan al’amarin, kamar yadda da dama suka ce ba laifi bane idan an binciki duk wanda ya aikata ko ake zarginsa da aikata ayyukan da absu dace ba.

Mahmud Ibrahim Kwari.

XS
SM
MD
LG