Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bincike Na Gudana Akan Hare Haren Mosul


Dakarun gamayyar da Amurka ke jagoranta a yakin ‘yan kungiyar Da’esh a Iraqi na gudanar da bincike akan rahoton Hare haren Jiragen sama da gamayyar takai a kwanan nan wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane fararen hula sama da 100 a unguwar Jidideh da ke Mosul.

A bayanin da gamayyar sojojin ta bayar tace “ mun bude binciken bayanan fararen hula na gaskiya sakamakon zargin.” Haka kuma bayanin yace Jiragen gamayyar na kai hare haren ne akan unguwannin da ‘Yan Daesh suke, sannan dakarun na gamayyar na daukar matakai na kulawa a yayin shirye shiryen kai hare haren ta jiragen sama domin kaucewa cutar da Fararen hula.”

Mai Magana da yawun tashar dakarun Amurka Col. John Thomas ya fadawa jaridar New York Times cewa, basu da masaniyar idan Bam din da ya fashe a yammacin Mosul ya faru ne sakamakon Dakarun Amurka ko kuma wasu daga cikin dakarun gamayyar ba, ko kuma tarko ne da ‘Yan Daesh suka d'ana.” Wani jami’n Iraqi yace yana da masaniyar abinda ya faru.Major General Maan Al-Saadi, kwamandan Dakarun Iraqi na musanman ya fadawa Jaridar The Times cewar, dakarunsa sun kira dakarun gamayyar ne na sojin sama domin su kare su daga wasu gwanayen harbi a kan gine gine guda uku dake unguwar ta Jidedeah a Mosul, Ya kara da cewa amma dakarunsa basu san cewar kasan gidajen makare yake da fararen hula ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG