Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Robert Mueller Ya Mika Sakamakon Bincikensa Ga Atoni Janar


Robert Mueller Barr
Robert Mueller Barr

Bincike na musamman na Robert Mueller ya kamala.

Bincike mai tsawo da aka dade ana jira game da katsalandan da Rasha ta yi a zaben shugaban kasa na 2016, da kuma ko shugaban kasar Amurka Donald Trump ya aikata ba daidai ba, abin da yasa sa ‘yan Majalisa sunyi ya yi kira da a saki rahoton binciken.

Mueller ya mikawa hukumar shari’a rahoton a jiya Juma'a, Babban Atoni Janar William Barr ya ke jagoranta, wanda a yanzu yake nazari a kai.

Manyan wakilan Majalisa na jam’iyyar Democrat sun ce, yana da "muhimmanci" a fitar da cikakken rahoton ga al’ummar kasar.

A cewar Sanata Chuch Schumer, na jam'iyyar Democrat, "Yanzu tun da mai bincike na musamman Mueller ya mika rahoton ga Babban Atoni janar, yana da muhimmanci ga Mr. Barr da ya fitar da cikakken rahoto ga al’ummar kasa, kuma ya bayar da takardun shaida da abubuwan da ke faruwa ga Majalisa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG