Yanzu da aka san abinda rahoton mai bincike na musamman Robert Muller ya kunsa, ana hasashe akan irin tasirin da sakamakon ya ke da shi akan siyasar Amurka gabanin zaben shugaban kasa dake tafe a shekarar 2020.
Takaitaccen bayanin rahoton wanda Atoni-janar na Amurka William Barr ya bayar, ya bayyana cewa mai bincike Mueller bai gano wata alaka ba tsakanin wadanda suka yi wa Trump yakin neman zabe da Rasha ba, na yin katsalanda a zaben shugaban kasa na shekarar 2016.
Amma Mueller bai yanke hukunci ba akan ko Trump ya nemi hana shari’a tayi aikinta dangane da binciken ko Rasha ta taka wata rawa a zaben ba ko a’a, a cewar Barr. Kuma duk da cewa rahoton bai bayyana cewa shugaba Trump ya aikata wani laifi ba, haka zalika bai kuma wanke shi ba.
A karshe, Barr ne yanke shawarar cewa hujjojin da Muller ya gano akan hana ruwa gudu wajen gudanar da binciken basu isa su sa a ci gaba da bincike akan batun ba.
Za ku iya son wannan ma
-
Janairu 25, 2023
Mawakiya Yar Najeriya Ta Yi Tarihi A Bikin Bada Lambar Yabo Na Oscar
-
Janairu 13, 2023
Lisa Marie Presley, Diyar Mawaki Elvis Ta Rasu
-
Janairu 11, 2023
Ana Tsaftace Yankunan Da Mahaukaciyar Guguwa Ta Ratsa A California
Facebook Forum