Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Birgediya Janar Julius Maado Bio Ya Lashe Zaben Shugaban Kasar Saliyo


 Julius Maada Bio, sabon shugaban kasar Saliyo
Julius Maada Bio, sabon shugaban kasar Saliyo

Biyo bayan kammala kidayar kuriun zabe zagaye na biyu Birgediya Janar Julius Maado Bio na jam'iyyar hamayya SLPP ya doke dan takarar jam'iyyar dake mulki yanzu

A saliyo, hukumar zaben kasar ta ayyana Birgediya Janar Julius Maada Bio mai ritaya, a zaman wanda ya lashe zaben shugabancin kasar zagaye na biyu. Maada dan jam'iyyar hamayya ta SLPP, watau Sierra Leone Peoples party, ya sami nasara ne da kashi 52 cikin dari na kuri'u da aka kada.

Shugaban hukumar zaben kasar Mohammed Conteh, wanda ya bayyana sakamakon zaben a daren jiya Laraba, yace dan takarar jam'iyyar dake mulkin kasar gabannin zabe, Samura Kamara, ya sami kashi 48 cikin dari.

Tuni dai aka rantsar da sabon shugaban kasar a daren jiya Laraba bayan da aka ayyana shi a zaman wanda ya lashe zaben.

A ranar 7 ga watan jiya ne aka yi zaben karo na farko, saboda babu dan takara da ya sami fiye da kashi 50 cikin dari na kuri'u da aka kada, aka tafi zagaye na biyu ranar 31 ga watan jiya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG