Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Birtaniya Za Ta Dauki Sojoji Daga Kasashen Da Ta Mulka


Wasu adakarun kasar Birtaniya

Tsarin da kasar ke bi shi ne, ‘yan kasar da Birtaniya ta mulka wadanda suka taba zama a kasar har na tsawon shekaru biyar ne kadai za su iya shiga rundunar sojin kasar.

Gwamnatin Birtaniya ta sanar da cewa daga yanzu ta bude kofar daukan sojoji aiki daga kasashen da ta mulka.

Sakataren tsaron Birtaniya, Gavin Williamson ne ya bayyana haka yayin wani taro da aka yi a yankin Salisbury.

Wannan sanarawa ta fito ne a daidai lokacin da Yarima Charles ke ziyarar wasu kasashen yammacin Afirka ciki har da Najeriya.

'Yan Najeriya da dama sun soki wannan mataki yayin da wasu ke yabawa.

Tsarin da kasar ke bi shi ne, ‘yan kasar da Birtaniya ta mulka wadanda suka taba zama a Birtaniya har na tsawon shekaru biyar ne kadai za su iya shiga rundunar sojin kasar.

Amma a wani mataki na kokarin daukan karin dakaru maza da mata a bangarorin sojin kasa da sama da na ruwa, ma’aikatar tsaron kasar ta soke wannan tsari.

Hakan na nufin 'yan kasar Birtaniyan ta raina kamar su Najeriya, Kenya, India da Australia za su iya shiga aikin soji a Birtaniya.

Wani rahoto da aka fitar a farkon shekarar nan, ya nuna cewa dakarun kasar ta Birtaniya sun gaza da sojoji 8,200.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG