Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Birtaniya Za Ta Mayarwa Da Iran Martani Kan Kwace Jirgin Ruwanta


Birtaniya na shirin daukan matakin kan Iran saboda kwace mata jirgin dakon manta da ta yi a Mashigin Hormuz.

A yau litinin Firai Ministan Birtaniya, Theresa May, za ta hadu da ministocin tsaro da jami’an tsaro don wata tattaunawa ta gaggawa kan yadda za su bullowa kwace jirgin ruwan dakon manta da Iran ta yi a yankin Mashigin Hormuz.

Daya daga cikin martanin da Birtaniya take tunanin dauka shi ne kakaba takumkuman karya tattalin arziki akan Iran. Ana sa ran nan gaba a yau May za ta yi wa ‘yan majalisar dokokin Birtaniya karin haske akan halin da ake ciki.

Wani faifan sauti da jami’an tsaron kan teku na kamfanin Dryad Global suka nada wanda aka sake shi a jiya Lahadi, an ji wani jirgin yakin ruwa na Birtaniya yana yin gargadi ga jami’an Iran da ke sintiri akan teku kan yin katsalandan ga jirign Birtaniya na Stena Impero yayin da yake ratsa mashigin na Hormuz.

Sai dai duk da haka dakarun juyin yuya hali na Iran sun sakko daga jirgi mai saukar ungulu inda suka kwace tankar dakon man jim kadan bayan da aka gargade su.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG