Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bisa Kuskure Jirginmu Ya Kashe Fararen Hula A Yobe – Sojojin Najeriya


Babban hafsan sojin saman Najeriya, Air Marshal Oladayo Amao (Facebook/NAF)
Babban hafsan sojin saman Najeriya, Air Marshal Oladayo Amao (Facebook/NAF)

A farkon 2017, wani jirgin sojojin Najeriya ya taba kai hari bisa kuskure akan wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke Rann a jihar Borno, inda mutane kusan 100 suka rasa rayukansu.

Rundunar sojojin saman Najeriya ta ce bisa kuskure ne wani jirgin yakinta ya bude wuta akan wasu fararen hula a kauyen Buhari da ke jihar Yobe a arewa maso gabashin kasar.

A ranar Laraba rahotanni suka nuna cewa wani jirgin yakin Najeriya ya kai samame akan wasu fararen hula a yankin, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum akalla takwas ya kuma jikkata wasu dama ciki har da kananan yara.

Da farko rundunar sojin saman ta Najeriya ta musanta kai wannan hari inda kakakinta Air Commodore Edward Gabkwet ya ce ba kamshin gaskiya a lamarin.

Sai dai a wata sanarwa da kakakin ya fitar a ranar Alhamis sojojin na Najeriya sun amsa cewa lallai wani jirginsu ya bude wuta a wani kauyen na Buhari da ke karamar hukumar Yunusari a jihar ta Yobe.

“A lokacin da jirgin namu yake shawagi a kudancin Kanama, ya lura da wasu zirga-zirga da ta yi kama da irin wacce mayakan Boko Haram kan yi, a duk lokacin da jirginmu ke shawagi.

“Sai matukin jirgin ya bude wuta. Yana da muhimmanci mu bayyana cewa, yankin, wuri ne da mayakan Boko Haram kan yi harkokinsu. Sai dai abin takaici, rahotannin da muka samu sai suka yi zargin cewa an kashe fararen hula bisa kuskure.”

Gabkwet ya kara da cewa, abin da ya sa suka musanta lamarin da farki shi ne, rahotannin da suka samu da bayan aukuwar lamarin sun nuna akasin hakan.

Rundunar sojojin saman ta Najeriya ta ce ta kafa wani kwamitin bincike don ya bi diddigin yadda wannan al’amari ya faru.

A farkon 2017, wani jirgin sojojin Najeriya ya taba kai hari bisa kuskure akan wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke Rann a jihar Borno, inda mutane kusan 100 suka rasa rayukansu.

XS
SM
MD
LG