Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bisa umurnin Buhari an tura kayan tallafi Borno wa 'yan gudun hijira


Shugaba Muhammad Buhari

Wani kwamiti a karkashin jagorancin babban hafsan sojojin Najeriya Janar Tukur Buratai ya kai Borno wasu kayan tallafi ma 'yan gudun hijira bisa umurnin shugaban kasa Muhammad Buhari

Babban hafsan sojojin Najeriya Janar Buratai ya mika kayan tallafin ne wa gwamnan jihar ta Borno Kashim Shettima.

Yayinda yake mika kayan ya yi bayanai yana cewa bari "na yi anfani da wannan damar na yaba maku saboda hadin kan da kuke bayarwa wajen samarda tsaro a sansanin".

Ya gargadesu kada su yi kasa a gwuiwa wajen bada rahoton wadanda basu yadda dasu ba wa jami'an tsaron sansanin saboda tsaron lafiyarsu da ma na wasu.

Kayan tallafin sun hada da buhuhunan shinkafa da mai da sabulu da sukari da sabbin tufafi hade da na gwanjo da kuma wasu ababen bukatu na yau da kullum. Za'a raba ma 'yan gudun hijiran bisa umurnin shugaban kasa Muhammad Buhari.

Gwamnan yace kayan da aka kawo masu ba'a bata kawo masu irinsu ba. Ya yi masu alkawari za'a raba kayan wa wadanda suka cancanta. Ya mika godiyarsu ga kwamitin da Janar Buratai da sojojin Najeriya da kuma uwa uba Shugaban Kasa. Yace Shugaba Buhari yana kaunarsu saboda haka kada su bari mayaudara su rudesu.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:54 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG