Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bisa Umurnin Kotu 'Yan sandan Israila Suna Rusa Gidajen 'Yan Share Wuri Zauna


Firayim Ministan Israila Benjamin Netanyahu
Firayim Ministan Israila Benjamin Netanyahu

Katafilolin 'yan sandan Isira'ila na shirin rusa gidaje da dama a yau dinnan Alhamis, bayan bai wa iyalan Yahudawa kimanin 50 da ke yankin share wuri zauna a Yamma da Kogin Jordan takardar sanarwa.

Daruruwan masu zanga-zanga sun kafa shingaye su ka yi ta jifar 'yan sandan da su ka zo aiwatar da umurnin kotun na kakkabe Amona, wanda wani matsugunin Yahudawa ne da ke arewa maso gabashin Ramallah, hedkwatar Falasdinawa.

Mafusatan masu zanga-zanga da 'yan share wuri zauna sun yi ta ihu ma 'yan sanda su na ta cewa, "Yahudawa ba su korar Yahudawa." An ji raunuka ma 'yan sanda kimanin 20, ciki har da wasu ma da su ka ce masu zanga-zangar sun watsa masu ruwan wani abi mai kona fuska.

XS
SM
MD
LG