Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kalamun John Kerry Sun Batawa Kafofin Labaran Israila Rai


Sakataren Harkokin Wajen Amurka, John Kerry
Sakataren Harkokin Wajen Amurka, John Kerry

Kafofin watsa labarai na kasar Isra’ila sun bayyana bacin rai da wasu kalaman da Sakataren-Harkokin-Wajen-Amurka, John Kerry yayi, wadanda suka bayyana da cewa “masu sukar rai” ne kuma “sun keta ka’idodin diplomasiya.”

Kafofin labaran na maida martani ne ga jawabin da Kerry yayi a gaban wani gagarumin taron da mafi yawan mahalartansa duk masu goyon bayan ita Isra’ila ne da aka yi a nan Washington inda, a cikin jawabin nasa, yake cewa ita kasar ta Yahudawa ta “kama hanya karere zuwa abkawa cikin hatsari” saboda manufofinta dangane da Palesdinawa.

Da yake amsa tambayoyin da wasu suka yi mishi a wajen wannan taron shekara-shekara na “Dandalin Saban” na Kungiyar Yahudawa da akayi a cibiyar Brookings, Kerry ya bayyana cijewar tattaunawar shirin sulhu tsakanin Isra’ila da Palesdinu da cewa ya sa abubuwa “sai kara cakudewa suke, kuma shirin ya chanja zuwa “wata alkibla da ba mai kyau” ba.

Jin haka ne jaridar Times of Israel, ta bayyana kalamin na Kerry da cewa “cin mutunci ne mai zafi.”

To amma Kerry ya bayyana cewa ai shima yana kaunar Isra’ila don a zaman da yayi kan kujerar SHWA, sau fiyeda 375 yana magana baki da baki da PM Isra’ila Benjamin Netanyahu, kuma ya je Isra’ila yafi sau 40.

Duk da haka, Kerry ya bayyana maganar da ministan ilmi na Isra’ila Naftali Bennet, yayi kwanan baya, inda yake yabawa da “mutuwar kokarin shirya sulhun tsakanin Yahudawa da Palesdinawa” da cewa “magana ce mai haifar da damuwa” sosai.

XS
SM
MD
LG