Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Nijar, An Shirya Taro Kan Biyan Haraji Da Ci Gaban Kasa


 Kungiyoyin fararen hula a Jamhuriyar Nijar
Kungiyoyin fararen hula a Jamhuriyar Nijar

Kungiyoyin farar hula sun shirya taron wayar da kawunan jama'a akan mahimmancin biyan haraji da ci gaba da gina kasa da hakkin da ya rataya akan kowane dan kasa da masu karbar harajin da gwamnati

A taron wayar da kawunan jama'a akan biyan haraji da aka yi a Damagaran, wani shugaban kungiyar Farar hula Nuhu Arzika ya yi kira su kula da abubuwan da yakamata su yi domin kyautata wa junansu da kasa.

Ya ce yakamata a fahimci matsalar biyan haraji da dalilin da ya sa dole a biyashi da kuma matsalar da ka iya kunno kai idan ba'a biyan haraji. Injishi dalili ke nan suka tara masana su fede wa jama'a biri har bindi akan biyan haraji da yin anfani dashi ta hanyoyin da suka kamata.

Gina kasa sai kowa ya hada karfi da karfe, inji Nuhu Arzika. Sai da gudummawar kowa da kowa ake iya gina kasa. Sai kuma an yi anfani da albarkatun dake kasa domin a samu abun biyan haraji da zai kaiga gina kasa.

Akan yadda yakamata a yi anfani da haraji, Nuhu Arzika na ganin idan bera nada sata to daddawa ma nada wari. Dole ne mahukumta su sa ido akan wadanda aka dorawa alhakin tattara haraji. A cewar Arzika mutanen Nijar na biyan haraji sai dai harajin na iya bin wata hanya daban. Ana iya karkatasu zuwa wata manufa daban da ba za ta anfani jama'a ba. Tana yiwuwa mutum ya biya haraji amma wanda aka bashi kudin ya ki kaiwa hukuma. Akwai kuma yadda masu karbar harajin ke karbar nagoro ba tare da karbar harajin ba. Injishi dalili ke nan mutane na biyan haraji amma basa gai a kasa.

Babban burin kungiyoyin hulan shi ne gwamnati ta dauki sandar ikonta a hannu ta kuma yi aiki da ita. Dole gwamnati ta yi gyara domin tabbatar da samun duk harajin da jama'a suka biya.

A cewar 'yan kungiyar fararen hulan duk dan kasa nagari dole ya ba kasa hakkinta, wato ya biya haraji saboda da harajin za ta yiwa jama'a aikin ci gaban kasa.

Ga rahoton Tamar Abari da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:09 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG