Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Blinken Ya Tattauna Da Takwaran Aikinsa Na Najeriya Onyeama


Sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken

Sakataren harkokin wajen Amurka Anthony J. Blinken, ya zanta da takwaran aikinsa na Najeriya Geoffrey Onyeama kan yadda Amurka ta dauki dangantakarta da kasar da muhimmanci.

A ranar Litinin, Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurkan Ned Price ya ce, a lokacin tattaunawar, Blinken ya zayyana irin yadda Amurka ke kallon dangantakar kasashen biyu bisa wasu muhimman batutuwa da suke mutuntawa kamar dimokradiyya, kare hakkin bil adama, da kuma dangantaka ta tsakanin juna da juna.

Blinken ya kuma yaba da nadin sabbin manyan hafsan sojojin kasar da shugaba Buhari ya yi don sauya irin yadda ake tunkarar ayyukan ta’addanci a arewa maso gabashi da tabbagtar da tsaro a sauran daukacin yankunan kasar.

Ministan Harkokin Wajan Najeriya, Mr. Geoffrey Onyeama
Ministan Harkokin Wajan Najeriya, Mr. Geoffrey Onyeama

Sakataren harkokin wajen na Amurka, ya yi nuni da yadda shugaba Biden ya soke takunkumi da aka sakawa Najeriya kan tsarin ba da visa, a matsayin wani mataki na nuna irin kusanci da ke tsakanin Amurkawa da ‘yan Najeriya.

Sannan ya jaddada goyon bayan Amurka ga Dr. Ngozi Okonjo Iweala a matsayin sabuwar shugabar kungiyar kasuwanci ta duniya WTO.

A farkon shekarar 2020 tsohon shugaba Donald Trump ya saka takunkumin visa akan Najeriya a sabon jerin sunayen kasashen da ya fitar wadanda aka hana su shiga kasar.

Dr Ngozi Okonjo-Iweala
Dr Ngozi Okonjo-Iweala

Amma bayan hawansa karagar mulki, shugaba Biden ya soke wannan doka da Trump ya saka.

Baya ga haka, gwamnatin Trump ta ki ba Najeriya goyon bayan a zaben shugaban kungiyar kasuwanci ta WTO inda ta gwammace ta goyawa ‘yar Korea ta Kudu baya.

Sai dai bayan hawan Biden mulki, ya sauya akalar tafiyar inda ya nuna goyon baya ga Najeriya kuma tuni har Dr. Okonjo-Iweala ta kama aiki a ranar 1 ga watan nan na Maris bayan da Amurka wacce ita kadai ta rage ta yi na’am da zabin Okonjo-Iweala.

An Ga Watan Azumi A Najeriya - Sultan

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammada Sa'ad Abubakar Ya Ba Da Sanrwar Ganin Watan Ramadan
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

An Kai Wa Ofisoshin Kungiyar Ba Da Agaji Hari A Arewa Maso Gabashin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:02 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG