Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Saki 'Yan Makarantar Kagara Da Malamansu


‘Yan bindiga sun saki yaran makarantar sakandaren kimiyar gwamnati ta Kagara da ke karamar hukumar mulkin Rafi ta jihar Neja.

Wani ma’aikacin gwamnatin jihar da ya bukaci a sakaya sunansa ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai tare da cewa, mutanen da aka sako na kan hanyar su ta zuwa Minna, babban birnin jihar ta Neja.

Nigeria Students Kidnapped
Nigeria Students Kidnapped

A cewar sa, ‘Yan bindigar sun saki yaran a kusa da inda suka saki mutane 53 da suka sace a makwannin baya, da wadanda suka sako a cikin makon jiya.

Ana sa ran gwamna Abubakar Bello na jihar ta Neja zai karbi mutanen da yan bindigar suka sako a fadar gwamnatin jihar da ke Minna.

Yaran makaranta 27 da saurian wasu mutane 14 ne ‘yan bindigar suka yi garkuwa da su daga makarantan.

Gabanin sakin daliban, gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya fadawa shirin “Sunday Politics” na gidan talbijin din Channels cewa an boye daliban a dajin Birnin Gwari.

Kalaman gwamman na zuwa ne sa’o’i bayan da aka kubutar da fasinjan motocin sufurin bas NSTA na jihar Nejar, wadanda wasu ‘yan bindiga suka yi awon gaba da su a ranar Lahadin wancan makon.

Najeriya dai ta jima tana fama da matsalar tsaro musamman a arewacin kasar, wacce baya ga rikicin Boko Haram take kuma yakar ‘yan bindiga da ke satar mutane domin neman kudin fansa, wadanda mafi aksarinsu rahotanni suke cewa Fulani ne.

Shehin Malami Dr Ahmed Gumi, ya yi ta yunkurin shiga tsakanin ‘yan bindigar da gwamnatin don a sasanta, lamarin da wasu ke suka yayin da wa suke yabawa.

Sheikh Ahmed Gumi Tare Da Fulani 'yan Bindiga
Sheikh Ahmed Gumi Tare Da Fulani 'yan Bindiga

Su dai ‘yan bindigar suna korafin cewa gwamnati ta yi watsi da su a al’amuranta suna masu cewa an bar su cikin dazuka suna wahala.

A ranar Juma’a shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce gwamnatinsa ba ta da niyyar ganin an rarrashi ‘yan bindigar yana mai cewa dalilin da ya sa ba su far masu ba shi ne, suna kiyaye dokokin yaki ne da aka kasashen duniya suka shimfida.

Sannan ana gudun kada a saka rayukan al’umar da ke cikin dazukan da wadanda ake garkuwa da su cikin hadari.

Daliban da aka sace da ke garin Kankara a jihar Katsina, Disamba 18, 2020​.
Daliban da aka sace da ke garin Kankara a jihar Katsina, Disamba 18, 2020​.

Sako daliban na Kagara, na zuwa ne kwana guda bayan sace dalibai sama da 300 da wasu ‘yan bindiga suka yi a makarantar sakandare ta kwana da ke Jangebe a karamar hukumar Talata Mafara a jihar Zamfara wadanda ake kan neman su.

Satar daliban na baya-baya nan ya sha suka daga Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar dinkin Duniya UNICEF, da sauran kasashen duniya.

Baya ga wadannan satar dalibai na Jangebe, a baya an taba garkuwa da daliban makarantar Chibok a jihar Borno, wadanda har yanzu ba a ga wasu daga cikinsu ba, da kuma na Makarantar Dapchi.

Leah Sharibu
Leah Sharibu

Har yanzu ba a saki wata daliba guda daya ba mai suna Leah Sharibu, wacce mayakan Boko Haram suka rike ta saboda rahotanni da suka ce ta ki zama Musulma.

Sai kuma daliban Kankara a jihar Katsina da na Kagara a jihar Neja da aka sako a yau.

Karin bayani akan: Shehin Malami Dr Ahmed Gumi, Kagara, Boko Haram, Nigeria, da Najeriya.

XS
SM
MD
LG