Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram Barazana Ce Ga Duk Afirka Ta Yamma Da Ta Tsakiya


Shugaba Idris Deby na Chadi, Shugaba Francois Hollande na Faransa, da kuma shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya a kofar dadar shugaban Faransa, Asabar 17 Mayu, 2014
Shugaba Idris Deby na Chadi, Shugaba Francois Hollande na Faransa, da kuma shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya a kofar dadar shugaban Faransa, Asabar 17 Mayu, 2014

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya kuma ya fadawa taron Paris cewa yanzu Boko Haram tana gararamba a zaman al-Qa'idar Afirka ta Yamma

Shugaba Frabncois Hollande na Faransa yace kungiyar Boko Haram ta Najeriya ta zamo barazana ga dukkan Afirka ta yamma da ta Tsakiya, kuma tilas a kafa wani tsari mai nagarta na yakarta.

Hollande ya bayyana wannan a wurin wani taron 'yan jarida yau asabar a Paris, a bayan wata ganawar da yayi da shugaban Najeriya da na kasashe makwabtanta.

Wannan taron na birnin Paris, ya biyo bayan satar dalibai mata su kimanin 300 da kungiyar Boko Haram ta yi daga wata makaranta. Jami'ai sun ce har yanzu akwai kimanin dalibai 276 a hannun tsageran na Boko Haram.

Shugaba Hollande yace Boko Haram kungiya ce mai alaka da al-Qa'ida, ya kuma fadawa shugabannin na Afirka cewa tilas ne a tsara wata dabarar musanyar bayanai da ayyukan hadin guiwa don murkushe kungiyar.

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya yarda, yana mai cewa "Boko Haram a yanzu ba kungiyar ta'addanci ta cikin gida ba ce kawai." Ya ce a yanzu tsageran su na gudanar da ayyukansu tamkar "al-Qa'idar Afirka ta Yamma."

Jonathan yace gwamnatinsa ta kuduri aniyar samo dalibai mata na Chibok da 'yan kungiyar suka sace. Yace an tura sojojin Najeriya dubu 20 zuwa arewacin Najeriya inda aka saci wadannan dalibai mata.
XS
SM
MD
LG