Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

BOKO HARAM: Kamaru Zata Girke Dakaru Kan Iyakar Kasar Da Najeriya


Babban Hafsan Sojojin Najeria Janar Tukur Yusuf Burutai Ya Ziyarci Sansanonin Sojojin Najeriya a Sambisa

Kasar Kamaru tace zata girke sojojinta a kan iyakar arewacin kasar da Najeriya da kuma iyakar yammacin kasar dake yankin masu amfani da harshen Ingilishi, biyo bayan wasu sababbin hare hare da Boko Haram suka kai a arewa da kuma yankin na ‘yan awaren kasar.

Ma’aikatar sojin Kamaru ta kira sojoji su taru a hedkwata a babban birnin kasar Yaoundé kafin babban aikin da zasu yi.
Babban hafsan ma’aikatar tsaro Lt. Gen. Rene Claud Meka yace a wannan shekarar ta 2019 Kamaru zata yi yaki domin hadin kan kasar da kuma tsare mutuncin iyakarta.
Yace sun sake girke dakarunsu a duk wuraren da ake samun tarzoma. Yace ‘yan ta’addan Boko Haram dake Najeriya suna kuma sake daukar mayaka daga Kamaru suna kuma kai hari a iyakar arewacin kasar. Yace a hali da ake ciki kuma ‘yan aware masu fafutukar ballewa daga yankin masu amfani da harshen Ingilishi su kuma suna daukar mayaka domin tada hargitsi a Kamaru.

Ma’aikatar sojin Kamaru tace Boko Haram tana sake gudanar da ayyukanta a kan iyakarta da Najeriya a arewacin kasar. Ta kuma bayyana cewa an kai hare hare sau biyar a kan iyakar da kuma tafkin Chadi a cikin wannan wata.
Mayakan ‘yan awaren kuma sun kara kaimi a yankunan masu amfani da harshen Ingilishi da suka hada da arewa maso yamma da arewa maso gabashin kasar. Sojan kasar tace an kashe ‘yan tawayen 45 a makwannin ukun farkon wannan shekara. Su kuma ‘yan awaren sun ce sun eke kashe sojojin.

Koda yake ba a iya bada takamammen adadi ba, amma mazauna kauyukan sun tabbatar da fadan ya kara ta’azzara a cikin wannan lokaci.

Wata ‘yar shekaru 27 da haifuwa tace an kashe ‘ya’yanta guda uku a cikin wani gagarumin fada a garin Buea dake kudu maso yammacin kasar kana bata san inda mijinta yake ba.
Tace wata motar daukar marasa lafiya ta ambulan mallakar wani asibitin cocin Katolika ce ta taimaka mata da wasu mata hudu ta arce dasu daga inda sojojin Kamaru da mayakan ‘yan awaren suka yi bata kashi.

Ana zargin ‘yan awaren da suke fafutukar ballewa a yankin masu amfani da harshen Ingilishi ne ta zama kasa mai cin gashin kanta da satar mutane da kashe abokan gaba da kuma kokarin hana gwamnati gudanar da ayyuka a yankunan.

Ministan tsaro Joseph Beti Assompo yace shugaba Paul Biya shi kuma ya bada umarni a jibge runduna a iyakar gabashin Kamaru. Yace fadan da ake gwabzawa a Jamhuriyar Tsakiyar Afrika yasa an samu karin miyagun ayyukan a wurin.

Yace wannan shekarar 2019 ba zasu yi bacci ba. Yace zasu ci gaba da ayyuka a arewa mai nisa da yankunan arewa maso gabas da arewa maso yamma da kuma sabonta ayyuka na musamma a yankin Adamawa, inda kungiyoyin miyagu na wurin suka kware wurin garkuwa da mutane da kuma neman kudin fansa.
Kasar Kamaru tace sama da mutane dubu daya da dari biyu aka kashe tun lokacin da rikicin ‘yan aware ya barke a shekarar 2016 kana wasu dubu dari biyu da hamsin suka rasa muhallansu.

Saurari cikakken rahoton da Baba Yakubu Makeri Ya karanta

Kamaru Zata Sake Salon Yakar Boko Haram-4:05"
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:19 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG