Accessibility links

Boko Haram Ta Kai Wani Sabon Hari A Kano

  • Aliyu Imam

Imam Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko-Haram.

‘Yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar nan ne dake da’awar Islama Boko Haram sun bude wuta kan wani caji ofis na ‘Yansanda cikin jihar Kano, wadda ya janyo musayar wuta.

‘Yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar nan ne dake da’awar Islama Boko Haram sun bude wuta kan wani caji ofis na ‘Yansanda cikin jihar Kano, wadda ya janyo musayar wuta.

Shaidu suka ce ‘yan bindigan da suka zo kan babura a yammacin jiya jumma’a sun bude wuta kan caji oifshin su kuma ‘Yansanda suka maida martani.

‘Yansanda basu gaskanta ko an sami wadanda suka jikkata ko ma mutuwa a wan nan harin.

Cikin makon jiya kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin kai hare harenda suka halaka mutane 185 a kano birni na biyu a girma aNajeriya.

Kamin a kai wan nan harin , shugaban kungiyar Imam Abubakar Shekau a sako da aka saka a internet, ya kalubalanci shugaba Goodluck Jonathan kan ikirari da yayi cewa gwamnatinsa zata kurkushe kungiyar

Ahalinda ake ciki kuma, an saki ba Amurken da aka sace a yankin Niger Delta mai arzikin mai, bayan an yi garkuwa da shi na mako daya.

Ofishin jakadancin Najeriya ya fada jiya jumma cewa mutumin da shekaru 50 d a haifuwa yana wani inda babu bazarana ga lafiyarsa. Ofishin bai bada bayanin yadda aka yi aka saki mutumin ba.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG